Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Bakiry wanda ya wallafa sako a shafinsa na Twitter ya kara da cewa; Bayan tsawon makwanni na tattaunawa, mun kusa cimma yarjejeniya a kowane lokaci daga yanzu, sai dai ba za a kulla yarjejeniya akan wani bangare ba, matukar ba a yarda da dukkan batutuwan da aka bijiro da su ba.
Tun a ranar 27 ga watan Disamba ne dai aka bude tattaunawa karo na 8 sai dai an rika samun tsaiko, inda wakilan kasashe su ka rika komawa gida domin yin shawarwari da gwanatocinsu.
342/